Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Sabuwar Shekara :2012


Wasan wuta a bikin shiga sabuwar shekara.

Shugaban Amurka Barack Obama da iayalinsa sunyi bikin shiga sabuwar shekara a Hawa’ii wurinda shine na karshe a doron kasa wajen ganin sabuwar shekara ta 2012.

Shugaban Amurka Barack Obama da iayalinsa sunyi bikin shiga sabuwar shekara a Hawa’ii wurinda shine na karshe a doron kasa wajen ganin sabuwar shekara ta 2012. Jihar Hawaii ce mahaifar shuagaban na Amurka.

Ana jin shugaban da iyalins a sunyi bikin shigar sabuwar shekarar a kadaice ta wasanni da irin kwarewar d a Allah ya baiwa wasu daga cikin iyalin nasa.

Fadar White House bata fadi wadanne irin wassani aka yi ba, sai dai an san uwargidansa Michelle Obama ta nuna kwarewarta a fannin wasu wasannin motsa jiki da na al’adar yankin na Hawa’ii.

Sa’o’I kamin nan, a birnin New York fitacciyar mawakiyar nan Lady Gaga, da Placido Domingo suna daga cikin jerin shahararrun mutane da suka yi nishanar tadda mutane a dandalin da ake kira Times Square, ind a aka yi kiyasin kamar mutane milyan daya suka halarci bikin.

A birnin Rio de jeneiro miliyoyin mutane ne suka je gabar ruwa da ake kira Copacabana domin kallon wasan wuta yayin da ake dakon shigar sabuwar shekara.

A wasu sassan duniya kamar Ingila, kasar da zata karbi bakuncin wasannin motsa jiki na Olympics a wan nan sabuwar shekara ta fara wasannin wutan ne da sake nuna hoton vidiyo lokacin da al’umar kasar suka sami labarin a Britaniya za a yi wasannin Olympics a wan nan shekarar. Dubun dubatan mutane ne suka ccirindo a gabar kogin da ake kira Thames domin kalllon wasan wutan.

Haka ma a birnin Berlin an yi gagarumin wasan wuta domin bikin shiga sabuwar shekara.

Kasashe dake yankin Asiya suna daga cikin rukuninkasashen farko da suka fara ganin sabuwar shekara. Sai dai bikin baiyi armashi ba ainun a binrin Tokyo sabo da juyayin girgizar kasa da igiyoyin ruwan tsunami da suka afkawa kasar cikin watan Janairun bara.

XS
SM
MD
LG