Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soma Ba Mutane Allurar Rigakafin Cutar Kwalara a Jihar Borno


Ma'aikatan kiwon lafiya a Borno suna ba mutane maganin rigakafin cutar kwalara

Gwamnatin Borno tare da hadin gwuiwar hukumar kiwon lafiya ta duniya sun soma ba mutane allurar rigakafin cutar kwalara a jihar a karon farko.

Gwamnatin jihar Borno tare da hukumar kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun kaddamar da allurar cutar kwalara a jihar Borno.

Allurar rigakafin ita ce irinta ta farko da za'a ba mutane a jihar da ma tarayyar Najeriya baki daya. Barkewar cutar amai da gudawa ko kwalara a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno ya sa aka soma ba da allurar.

Tun a ranar 16 ta watan Agustan wannan shekarar ce aka samu barkewar cutar a daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira. Alkalumma sun nuna cewa kimanin 2617 ake kyautata zaton sun kamu da wannan cutar. Haka ma wasu 47 sun rasa rayukansu.

An samu bullar cutar ne a kananan hukumomin guda uku sakamakon wani gwajin da aka yi a sansanonin amma mafi yawan mace macen ya auku ne a garin Maiduguri sakamakon cutar.

Bayan kaddamar da allurar wadda Mataimakin gwamnan jihar Usman Mamman Dikwa ya yi wanda kuma shugaban ma'aiatan gwamnatin jihar Architect Yerima Saleh ya wakilta, ya bayyana mahimmancin allurar. Yana mai cewa duk wanda ya samu allurar ya samu kariya daga cutar. Ya kira 'yan IPDs da su fito su karbi maganin. Su ma shugabannin gwamnatin jihar sun karbi allurar

Dr Haruna Mshelia kwamishanan ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar yana mai cewa allurar sabuwa ce. Ba'a taba ba kowa a Najeriya ba sai wannan karon. A cewarsa kashi tamanin na duk wadanda suka samu allurar ba zasu kamu da cutar ba bisa ga sakamakon gwajin da aka yi.

Yanzu dai an shawo kan cutar domin matakan tsaftacewa da gwamnatin ta dauka inji kwamishanan kiwon lafiyar jihar.

Wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya yace allurar na cikin matakan da suka dauka domin shawo kan cutar a Borno kuma zasu cigaba da sauran matakan.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG