Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Masu Safarar Makamai Hukuncin Daurin Shekaru 5 A Gidan Yari

Azim Aghajani, dan asalin kasar Iran da abokinsa na Najeriya Usman Abbas Jega sun karbi hukuncin shekaru 5 a gidan yari yau Litinin saboda samun su da akayi da laifin kitsa safarar makamai irin na Soji zuwa yammacin Afrika. Duka mazan guda biyu sun roki da’a sassauta musu hukuncin, inda ma Alkali Okechukwu J. Okeke ya rangwanta basu daurin rai da rai. Azim Aghajani da Usman Abbas Jega sun riga sun share shekaru 2 a gidan yari, kuma za’a tara wa’adin shekarun da suka riga suka yi a rike, da na hukuncin da aka yanke musu.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG