Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Cika shekaru 242 Da Samun ‘Yancin Amurka a Abuja


Jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington da wakiliyar gwamnatin Najeriya wurin bikin Jakadiya Adebiyi

Ofishin jakadancin Amurka ya gudanar da bikin cika shekara 242 da samun ‘yancin Amurka wanda ya samu halartar dimbin jama’a da suka hada da gwamnan jihar Kaduna

Jakadan Amurka a Najeriya Ambasada Stuart Symington ya nuna damuwa bisa yadda ake samun karuwar kashe kashe tsakanin ‘yan Najeriya.

Da yake jawabi a wani Gagarumin bikin murnar zagayowar ranar da Amurka ta samu ‘yanci, da aka yi a Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja, Ambasada Symington ya ce wadannan kashe kashe da ake yi ba za su haifarwa kowa kome ba hasali ma rashin kyautawa ne haka kurum ayi ta zubadda jinin mutanen da basu san hawa ba balle sauka.

Ya ce shugabanni da wasu ‘yan Najeriya, zasu iya dakatar da wannan kashe kashe nan take muddin aka yi aiki tare, ba tare da yin la'akari da bangaranci ko banbancin addini ba.

Jakadan na Amurka ya ce kasarsa tana aiki kafada da kafada da Najeriya wajen tabbatar da ci gaba. Suna yaki da cututtuka don ceto rayukan jama'a da ma fatattakar jahilci da talauci tsakanin ‘yan kasa.

Gwamnan jihar Kaduna da shi ma ya halarci taron ya ce dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka na da kyau sosai, inda ya yi tilawar yadda Shugaba Donal Trumph ya amince a saidawa Najeriya manyan jiragen yaki na zamani. Ya yi hakan don baiwa sojojin Najeriya damar gaggauta kawo karshen tarzomar ‘yan ta'adda na Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Taron dai ya sami halartar ‘yan Najeriya daga sassan kasar, da jami'an diflomasiyyar kasashen duniya dake Abuja, da kusoshin gwamnati da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa. Dalibai da malaman Jami'o'i da jami'an tsaro ma ba’a barsu a bay aba.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG