Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Kasa Yayi Hadari A Jebba Jihar Kwaran Najeriya


Wani taragun jirgin kasan da yayi hadari kan hanyar zuwa kano daga Legas, raenar Asabar.

Jirgin kasan wanda yake hanyar zuwa kano, ya taso ne daga Legas.

Rahotanni wadanda ba'a tabbatar ba daga yankin sunce, hadarin ya kashe mutane masu yawa. Amma kakain rundunar 'Yansandan jihar ASP Ajayi Okasanmi, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa, a saninsa mutane hudu ne suka mutu zuwa lokacinda ya aiko da wannan rahoto.

Shaidun gani da ido sun gayawa wakilin Sashen Hausan cewa, taragan jirgin hudu ne suka kauce hanya, kuma akwai mutane masu yawa wadanda jirgin ya danne.

Sarkin Jebba, Alhaji Indama Mohammed, yace wadnada suka mutu suna da yawa, kuma hukumomi sunce an tada jirgi da kayan aiki daga Legas, wanda zai zo ya tada taragan, amma zuwa lokacinda suka yi magana, jirgin bai kai can ba tukun.

Shima wani mazaunin garin, Suleman Jebba, ya gayawa wakilin namu cewa, an kai wadanda suka jikkata wani asibiti da ake kira katamaya, tareda gawarwakin wadanda suka mutu.

Yace masu aikin ceto, ciki harda jami'an hukumar kiyaye hadura ta Najeriya watau Road Safety, suna gudanar da agajin gaggawa a wurin da jirgin ya kauce hanya.

Nan take dai babu bayanai kan abunda ya haddasa hadarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG