Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-Zangar Lumana A Filato


Wasu Mata da suka yi zaman dirshan a Nijar
Wasu Mata da suka yi zaman dirshan a Nijar

Yayin da sassan Najeriya ke fama da tashe-tashen hankula, kungiyoyin mata na yankin tsakiyar Najeriya sun yi zanga-zangar lumana a birnin Jos saboda kiran hukumomi su tabbatar da zaman lafiya.

A wani al’amari na neman jaddada zaman lafiya da cigaba a jahar Filato, kungiyoyin mata na yankin tsakiyar Najeriya sun yin zanga-zangar lumana a harabar Majalisar Dokokin jahar Filato yayin gabatar da kokekokensu don gwamnati ta dau mataki a kai ta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin saboda manoma su samu sukunin nomansu da kuma komawa gidajensu.

Sakataren Yada Labaran Kungiyar Matasan Yankin Tsakiyar Najeriya Arise Clement Selbong y ace dole ne gwamnati ta kuduri aniyar kawo karshen kashe-kashe a yankin. Wata shugabar mata daga Karamar Hukumar Bokkos mai suna Julia John Mangai ta ce akasarin manoma sun rasa muhallansu don haka ya kamata gwamnati ta mayar da su gidajensu.

Kakakin Majalisar Dokokin jahar Filato Peter Azi ya ba su tabbacin cewa Majalisar za ta mika kokensu ga hukumomin da abin ya shafa.

Ga wakiliyarmu Zainab Babaji da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG