Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Fursunoni Afuwa a Kaduna


Dakin Gidan Yarin da aka kulle tsohon shugaban Afrika ta kud Nelson Mandela

Gwamnan Jahar Kaduna, Malam Nasiru El Rufa’I, ya yiwa wasu fursunoni afuwa albarkacin bikin cikar Najeriya shekaru 55 da samun yancin kai yayin da aka ragewa wasu yawan wa'adin da aka yanke musu.

Bisa al’ada shugabannin musamman gwamnonin juhohi sukan yi afuwa ga wasu fursunoni, inda a ranar Alhamis gwamna El Rufa’I ya yi alkawarin sakin wasu fursunoni

A kuma yau Litinin ne, gwamnan ya cika wannan alkawarin inda aka saki fursunoni maza da mata daga gidan yari.

Baya ga sakin wasu fursunoni, an kuma ragewa wasu daga cikin yawan shekarun da aka diba musu albarkacin wannan rana.

“Sharri ne aka min na maita, kuma shekaru biyu aka bani, na ji dadi na kuma gode” In ji wata mata da aka saka mai suna Nawa daga Saminaka.

Shi kuwa Muhammed Usman daga Zaria cewa “Laifi nay a shafi maganar addini ne, shekara biyu aka daure ni, lallai ina godiya ga gwamna da ya taimaka mana, kuma Allah ya taimake shi.”

Babban Comptroller gidan yari da ke jahar ta Kaduna, Abubakar Garba Talban Kebbi, ya ce, kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa gwamna damar yiwa wasu fursunoni afuwa.

“Mutanen da aka ga sun canja halayensu a sake su. Sai dai akwai fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa wadanda ba ‘yan jahar Kaduna ba, wadannan gwamna ba shi da ikon ya ce a sake su.”

Ga karin bayani a wannan rahoto na Nasiru Yakubu Birnin Yaro:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG