Accessibility links

An Zabi Saneta John Kerry Ya Maye Gurbin Hillary Clinton


Saneta John Kerry, D-Mass.
Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Saneta John Kerry a matsayin wanda zai karbi matsayin sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Shugaba Obama ya bayyana a fadar White House jiya jumma’a cewa, Kerry shine mutumin da ya dace da jagorantar harkokin diplomasiyan Amurka a cikin shekaru masu zuwa. Bisa ga cewarsa, Kerry yana da kima a idon abokansa ‘yan majalisar dattijai da kuma shugabannin kasashen duniya sakamakon ayyukan da yayi na tsawon shekaru da dama.

Shugaba Obama ya bayyana cewa, akwai kalubalai da dama a gaba, sai dai ya kakikanta cewa, Amurka zata ci gaba da jagoranci.

Kerry, dan jam’iyar Democrat daga jihar Massachussetts ya yi aiki a matsayin shugaban kawamitin harkokin kasashen ketare a majalisar dattijai, ya kuma yi tafiye tafiye da dama zuwa kasashen da ake fama da tashin hankali daga Afrika zuwa Pakistan. Shi kuma tsohon soja ne wanda ya sami lambar yabon yakin Vietnam.

Kerry dan shekaru 69 da haihuwa, ya tsaya takarar shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da hudu, zaben da shugaba George W. Bush ya lashe.

Idan majalisar dattijai ta amince da zabensa, Kerry zai gaji sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka mai ci yanzu, Hillary Clinton, wadda ta bayyana cewa, ba zata ci gaba da rike wannan mukamin ba a wa’adin mulkin Mr. Obama na biyu.
XS
SM
MD
LG