Accessibility links

Ana Fuskantar Mummunar Ambaliyar Ruwa A Makurdi


Hoton wani gida ya kusan nutsewa baki daya cikin ruwan ambaliya a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai

Ruwa ya malale unguwannin dake bakin kogin Binuwai a babban birnin na Jihar Binuwai

Dubban jama’a dake zaune a unguwannin da suke bakin kogin Binuwai a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, su na gudu daga cikin gidajensu, a bayan ambaliyar ruwan dake kara yin muni kullum.

A cikin hirarsu da Ibrahim Alfa Ahmed, Malam Tijjani Mohammed, manajan gidan mai na NNPC Mega Station dake Makurdi, yace yanzu sai da jiragen kwale-kwale ake iya zirga-zirga a duk tsawon bakin kogin na Binuwai, ya kuma bayyana yadda harkokin yau da kullum suke gudana a can...
XS
SM
MD
LG