Accessibility links

Ana ci gaba da gumurzu a kasar Siriya


wadansu mata da aka kai hari a unguwarsu
’Yan gwaggwarmayar kasar Siriya sun ce dakarun shugaba Bashar al-Assad sun bude wuta a wadansu sassan babban birnin kasar da kuma birnin Aleppo inda ake fama da tashin hankali yau jumma’a, kwana daya bayanda Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin kawo karshen aikin gani da ido da take yi a kasar.

Kungiyar kare hakkin bil’adama kan harkokin kasar Siriya dake da zama a Birtaniya ta kuma bada labarin arangama tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawaye kusa da babbar tashar jirgin saman sojin kasar dake Damascus.

Rami Abd-al-Rahman, darektan cibiyar sa idon ta Birtaniya ya shaidawa Muryar Amurka cewa, tashin hankali na baya bayan nan ya auku ne bayan kashe a kalla mutane 180 jiya a duk fadin kasar. Yace an sami gawarwakin wadansu mutane 65 da ba a tantance ba, a garin Qatana dake kudu maso yammcin birnin Damascus.

Jiya alhamis, kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa, zai bar wa’adin aikin masu gani da ido a Siriya ya cika. Ranar Lahadi ne wa’adin yake cika, sai dai kwamitin Sulhu yace yana kyautata zaton kafa ofishi a kasar da yaki ya daidaita.

Shugaban Kwamitin a halin yanzu, jakaden kasar Faransa, Gerard Araud yace, membobin kwamitin sun amince da cewa, ba a cika sharudan da aka gindaya da zai bada damar ci gaba da aiki a kasar ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin Siriyawa miliyan biyu da dubu dari biyar suna bukatar agaji sabili da tashin hankalin da aka shafe watanni goma sha takwas ana yi na nuna kin jinin Mr. Assad.
XS
SM
MD
LG