Accessibility links

Ana matsawa kasar Gambiya lamba ta daina aiwatar da hukumcin kisa


Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh
Gambiya tana kara fuskantar matsin lamba a kan ta dakatar da aiwatar da hukumce-hukumcen kisa, yayin da fargaba ke karuwa kan cewa gwamnati zata kashe fursunoni masu yawa cikin ‘yan makonnin da suke tafe.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce tilas shugaba Yahya Jammeh na Gambiya ya janye barazanar da yayi ta zartas da hukumcin kisa a kan dukkan fursunonin da aka yanke musu irin wannan hukumci a kasar, tare da dakatar da aiwatar da duk wani hukumcin kisa a kasar.

Da maraicen jiya talata ma, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kiran da a gaggauta kawo karshen zartas da hukumcin kisan, tana mai bayyana damuwa da kashe fursunoni 9 da kasar Gambiya ta ce ta yi ranar litinin.

Gambiya ta ce an zartas da hukumcin kisa a kan fursunoni 9, cikinsu har da mace daya da wasu ‘yan kasar Senegal biyu, sai dai an samu sabanin ra’ayi a kan lokacin da aka aiwatar da hukumcin.

Yau laraba, firayim ministan Senegal, Abdoul Mbaye, yayi sammacin jakadan Gambiya inda ya bayyana masa rashin yardarsa dangane da yadda aka zartas da hukunmcin cikin sirri.

Yace tilas ne a kare hakkokin sauran ‘yan kasar Senegal da ake tsare da su a kasar ta Gambiya.
XS
SM
MD
LG