Accessibility links

Anyi Bikin Tuni Domin Kulawa Da Ruwa Ta Duniya

  • Aliyu Imam

Dan Adam yana shan kimanin ruwa lita uku ako wace rana.

Jiya laraba aka gudanar da bikin tunawa da ranar muhimmancin ruwa ga Bil Adama, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ke karfafa wayar da kan al’ummar kasa da kasa.

Jiya laraba aka gudanar da bikin tunawa da ranar muhimmancin ruwa ga Bil Adama, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ke karfafa wayar da kan al’ummar kasa da kasa irin muhimmancin da samar da ruwan sha ga al’umma ke dashi.

Yayin da ake wnanan bikin tunawa da ranar ruwan sha ne al’ummar kasar Kenya ke gargadin cewa da alamar zasu shiga uku muddin ruwan tafkin da suke diba ya kai ga kafewa. Alamar kafewa tazo ne kwanaki kadan kafin ranar bikin a wani tafkin da mazauna Nairobi ke samun ruwa bayan sun bi dogon layi domin cika jarkar lita 20 har kokawa mata da kananan yara keyi domin samun ruwa.

Cece-kucen da ake yawaita yi ke nan wajen diban ruwan sha a tafkin Nairobin kasar Kenya. Shin me ya janyo haka ne, wani jami’in dake kula da tafkin yace saboda tafkin na samar da ruwan sha mai kyau da tsafta. Gefe guda kuma an sami wasu jami’an da suka giggina rijoyin burtsatse domin su rika saida ruwa ga jama’a. Peter Njeru, na daga cikin masu irin wadannan rijiyoyin burtsatsen a Kibera.

Peter Njeru yana mai cewa karfa a manta idan babu ruwa Dan Adam zai hadu matsaloli da yawa domin ba za’a iya dafa abinchi ba, ba kuma za’a iya wanka da wanki ba, kai ba abinda za’a iya yi im babu ruwa, don haka ruwa shine rayuwar Bil Adama.

XS
SM
MD
LG