Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi jana'izar Albertina Sisulu a Afrika ta kudu


Anyi jana'izar Albertina Sisulu a Afrika ta kudu

Tsohon shugaban Afrika ta kudu, Nelson Mandela ya baiyana Albertina Sisulu a zamar daya daga cikin yan kasar Afrika ta kudu da ba za’a taba mancewa da ita ba a saboda gudumawar data bayar wajen yaki ta mulkin wariya

Tsohon shugaban Afrika ta kudu, Nelson Mandela ya baiyana Albertina Sisulu a zamar daya daga cikin yan kasar Afrika ta kudu da ba za’a taba mancewa da ita ba a saboda gudumawar data bayar wajen yaki ta mulkin wariya. Tsohon shugaban yayi wannan furuci ne a yayinda yan kasar suke yiwa wannan mace karamawa ta karshe a wajen jana’izarta a Soweto a yau asabar. Matar Mandela, Graca Machel itace ta karanta wannan sako na Mandela a madadinsa.

Tsohon shugaba Mandela yace ba zai iya zuwa jana’zar ba a saboda tsanin bacin ran rasuwar wannan mace. Mr Mandela shine abokin ango a lokacinda Albertina ta auri Walter Sisulu daya daga cikin wadanda suka yaki mulkin wariya a kasar. A lokacinda gwamnatin wariya ta jar fatar Afrika ta kudu suka garkama Walter Sisulu da Mr Mandela a gidan yari a alif dari tara da sittin da hudu, sai Albertina Sisulu ta fara wannan aiki na mijinta na yaki da mulkin wariya. Za’a bizne ta kusa da kabarin mijinta a Soweto. Albatina wadda ake kira Mama Sisulu ta mutu ne a gidanta a birnin Johanesburgh a ranar biyu ga wannan wata na Yuni tana da shekaru casa’in da biyu a duniya.

XS
SM
MD
LG