Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 24 Da Aka Yi A Jihar Nija.


Zaben 2015: Ma'aikatan zabe na shrin kayan aiki

Yayinda jam'iyya mai mulki tage murna, 'yan hamayya suna cewa suna da ja.

A karshen mako ne gwamnatin jihar Nija dake arewa maso tsakiyar Najeriya, ta gudanar da zaben kananan hukumomi da suke jihar.

Hukumar zabe ta jihar, ta ayyana jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta Nija, a zaman wacce ta lashe zaben. Amma 'yan hammayya sunce ba'a gudanar da zabe ba.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar, Bello Agwara, yace a cikin mazabu 56 da suke karamar hukumar Agwara, 36 duk ba'a kai akwatunan zabe ba. Saboda haka ne yace su zasu rubuta rahoton cewa su bada jam'iyyar aka yi zaben nan ba. Domin haka ne ma suka ki zuwa hukumar zaben baki daya.

Shima dan takara a inuwar jam'iyyar PDM Rabi'u Tasi'u, yace an kori wakilan jam'iyyar a mazabun da suke karamar hukumar kontagora, sannan aka yi awon gaba da wasu kawatunan zabe.

Amma da yake magana lokacinda yake kada kuri'arsa ranar Asabar, Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yaba da yadda ake tafiyar da zaben.

Ahalinda ake ciki kuma, rundunar 'Yansandan jihar Nijan ta kama mutane 100 dangane da laifuffukan zabe. Kakakin rundunar Bala Elkanah yace suna kammala shirye shirye domin gurfanar da su a gaban kotu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG