Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ashraf Ghana ne Sabon Shugaban Kasar Afghanistan


Ashraf Ghani Shugaban kasar Afghanistan.

Afghanistan ta kaddamar da Ashraf Ghana a matsayin sabon Shugaban kasar, a wani bikin da ake yabawa a zaman sauyin gwamnati a dimokaradiyyance a karon farko a kasar.

Afghanistan ta kaddamar da Ashraf Ghana a matsayin sabon Shugaban kasar, a wani bikin da ake yabawa a zaman sauyin gwamnati a dimokaradiyyance a karon farko a kasar.

Cikin tsauraran matakan tsaro, wakilai hukumomi daga sassan duniya su ka bi sahun 'yan siyasa da shugabannin addini a Afghanistan wajen wannan biki na yau Litini, wanda aka yi a Fadar Shugaban kasa da ke birnin Kabul.

Ghani, wanda ya taba zama Ministan Kudin kasar na tsawon shekaru biyu karkashin Shugaba Hamid Karzai mai barin gado, ya gayyaci kungiyoyin adawa - ciki har da Taliban - don a tattauna kan makomar kasar.

Ya ce, "Fada ba shi ne hanyar warware bambamcin siyasa ba, mun nuna wa duniya cewa za a iya warware bambamcin siyasa ta tattaunawa a siyasance. Don haka ina kira ga masu adawa da gwamnati - musamman ma Taliban da Hezb-e-Islami su shiga tattaunwar a siyasance."

Abokin karawarsa a zaben, Abdullah Abdullah, shi ma an rantsar da shi a matsayin sabon babban jami'in zartaswa na kasar, bisa ga wata yarjajjeniyar raba iko, wadda aka cimma bayan tashin hankalin bayan zabe, wanda aka yi wata da watanni ana yi.

To saidai wannan rana ta kaddamarwar ba ta barata daga tashin hankali ba. Kungiyar Taliban ta dau alhakin kai wasu hare-haren kunar bakin wake daura da filin jirgin saman Kabul, da su ka kashe mutane akalla hudu.

XS
SM
MD
LG