Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Attahiru Jega Shi Ne Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Najeriya


Attahiru Jega

Wani babban jami'in gwamnati a Najeriya ya ce an nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, INEC.

Wani babban jami'in gwamnati a Najeriya ya ce an zabi wani tsohon shaihin malami na jami'a ya zamo sabon shugaban hukumar zabe ta kasar.

Gwamna Adams Oshiomhole ya fada cewa a yau talata aka zabi Farfesa Attahiru Jega domin ya zamo shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta, INEC, ba tare da hamayya ba.

Yanzu za a mika sunan Farfesa Jega ga majalisar dattijai domin neman amincewarta.

Farfesa Jega, wanda tsohon shugaban Jami'ar Bayero ta Kano ce,l ya taba zamowa mai bayar da shawara ga hukumar ta INEC a can baya.

Masu sukar lamiri sun bukaci Najeriya da ta aiwatar da sauye-sauyen zabe, tare da yin garambawul a hukumar ta INEC kafin zaben shugaban kasa na 2011.

A shekarar 2007, Najeriya ta mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata gwamnatin ta farar hula a karon farko a tarihin kasar. Amma 'yan kallo sun ce an tabka magudi mai yawa tare da tashin hankali da cin zarafin abokan hamayya a lokacin zaben na 2007.

XS
SM
MD
LG