Accessibility links

Biyo bayan hadarin jirgin kasa da ya auku a Legas hukumar jirgin kasa ta sallama sabanin boye-boyen da ake yi da.

Ba kasafai hukumar jirgin kasa ke barin a bayyana hadarin jirgi ba wai domin kada mutane su shiga wani halin bakin ciki.

Biyo bayan hadarin da aka yi kuma har ya lakume rayuka tara tare da na matukin jirgin da mataimakinsa yanzu hukumar kula da harkokin jiragen kasa ta daina boye-boyen da ta saba yi can baya dangane da hadarukan jiragen a Najeriya.

Wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya samu ya zanta da Barrister Ibrahim Jalo daya daga cikin shugabannin hukumar jiragen kasa. Da aka tambayeshi dalilin da yasa hukumar ta hana mutane shiga inda jirgin kasan da yayi hadari sai yace abun da yake da kyau ake son a fada amma ba mummunan labari ba. Yace kullum abun da 'yan Najeriya ke son ji shi ne abun farin ciki ba na bakin ciki ba.

Dangane da dora wani a aikin harkokin jirgin kasa wanda bai san hawaba balle sauka lamarin da wasu suka ce yana cikin dalilan da suke jawo hadari sai Barrister Ibrahim Jalo yace shi ya san daraktan kuma a karkashinsa yake aiki. Ban da haka kwararre ne.

Game da dalilin musabbabin wannan hadarin Ibrahim Jalo yace akwai abu guda biyu. Na farko idan aka zuba yayi akan hanyar jirgin ko ledodi watakila jirgi na iya samun hadari. Na biyu matukin na iya shiga wani yanayi da ka iya kaiga hadari. Amma abun da ya tabbata ikon Allah ya shige komi da ake zato.

Shi dai wannan jirgin da ya yi hadari ya samu matsalar birki ne tun gada garin Ibadan har zuwa Abeokuta kana zuwa Legas inda ya zarce ya bankade wani gida.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.
XS
SM
MD
LG