Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Balaguro daga Legas zuwa Kano akan jirgin kasan Ooni of Ife

Najeriya ta sake bude hanyar jirgin kasanta zuwa arewacin kasar ran 21 ga watan Decemba, lamarin da ya kawo karshen aikin dala miliyan 166 da akayi amfani dashi wajen gyara hanyar da ta dade da lalacewa. Kamfanin gwamnatin Chana mai suna China Civil Engineering Construction Corporation ne ya gyara hanyar jirgin dake yankun kudancin Najeriya, sannan wani kamfani a Najeriya ya gyara ragowar. Gyaran layin ya kawo sassaucin sufuri ga talakawa, wadanda ke kokarin tafiya zuwa wurare a kasar, duk da cewa kudaden da mutane suke samu bai fi dala 1 a rana ba. Hawa jirgin sama na da tsada, kuma yawo a cikin mota a kan mutattun titunan kasar na da hadari. Tikitin jirgin kasa mafi sauki yana kama misalin dala 13.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG