Accessibility links

Bankin Duniya Zai Ba Jihar Oyo Lamunin Dala Miliyan 200


Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim

A wani kokari na shawo kan ambaliyar ruwa da jihar Oyo ke fama da shi kowace shekara bankin duniya ya yadda ya ba jihar lamunin dalar Amurka miliyan dari biyu.

A kokarin da gwamnan jihar Oyo ke yi na kawo karshen ambaliyar ruwa, bankin duniya zai baiwa jihar bashin dalar Amurka miliyan dari biyu. Ita ma jihar zata bada kason dala miliyan ashirin.

Za'a kashe kudin ne wurin gina hanyoyin hana ambaliyar ruwa a jihar. Shugaban bankin a Najeriya Dr Elanus shi ya furta hakan a lokacin da ya kaiwa gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ziyara. Shugaban bankin ya kara da cewa suna fatan baiwa jihar labari mai dadi bayan taron daraktocin bankin da zasu yi ranar 27 ga watan Mayu inda zasu tattauna batun lamunin.

Yace dangane da lamunin za'a sanya masu sa ido wadanda ba 'yan jihar Oyo ba ne kuma ba ma'aikatan bakin duniya ba ne domin su tabbatar an yi anfani da kudin kan ayyukan da aka karbi lamunin. Su masu sa idon ne zasu sanarda bankin duniya da ma gwamnatin ta Oyo kan yadda aikin ke gudana.

Gwamnatin jihar ce ta nemi lamunin sabili da ambaliyar ruwa da take fama da shi kowace shekara. Idan ba'a manta ba a watan takwas na shekarar 2011 jihar ta yi fama da wani mugun ambaliyar ruwa da ya lakume rayuka sama da dari. Haka ma makarantu da masana'antu da hanyoyi da kasuwanni da ababen hawa suka salwanta a ambaliyar ruwan.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
XS
SM
MD
LG