Accessibility links

Bankin raya kasashen Asiya ya gargadi kasashen yankin kan yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa


JWani mutum a inda aka yi ambaliyar ruwa cikin watan Janairu a Rockhampton,
Wani sabon rahoton da babban Bankin Raya Kasashen Asia (ADB) ya fito da shi na jan kunnen manyan biranen nahiyar da cewa lalle su tashi tsaye su fara daukan matakan inganta yanayinsu in ba haka ba kuwa zasu zo su fara fuskantar bala’oi kamar ambaliyar ruwa da mummunar nakkasar yanayin da ba zasu iya sarrafa ta ba. Rahoton yace nahiyar Asia, wacce yanzu a duk duniya ba nahiyar da garuruwanta da alkaruyu ke kara bunakasa kamar nata, yanzu haka itace take da fiyeda rabin mutanen duniya mazauna birane da alkaryu. Nan da shekaru goma masu zuwa, ana kiyasin cewa 21 daga cikin birane mafi girma 37 da ake da su a duk duniya, zasu kasance a cikin nahiyar ta Asia ne. Sai dai bankin na ADB yace wannan bunkasar ta manyan garuruwan tazo da tsada don ta haifarda lalacewar yanayi, kazaman unguwanni da kuma banbaci a tsakanin karfin arzikin dake ga mutane, da na kayan aikin inganta rayukkan wa’anda ke zaune a nan da wa’anda ke zaune a can.
XS
SM
MD
LG