Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boma Bomai Sun Tashi A Birnin Maiduguri


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Mun sami labarin an sami fashe fashe a wurare daban daban a bnirnin Maiduguri da misalin azahar a wunin Yau.

Rahotanni da muke samu daga Maiduguri babban birnin jihar Maiduguri, yana nunin cewa an sami fashe fashe daban daban cikin birnin, ciki har da babban sakatariyat ta jihar, sa'a daya bayan da sabon Gwamnan jihar, Alhaji Kashim ya kai ziyarar aiki a sakatariyar.

Wakilin Sashen Hausa yace masu buga musu woya sun bada labarin cewa, fashe fashen sun kuma auku a wasu ofisoshin 'Yansanda dake unguwar Gwange da kuma Dandal Way, dake cikin birnin.

Masu buga woyar sun kuma bada labarin jin harbe harben bindiga bayan tashin abubuwan da ake kyautata zaton boma bomai ne.

Hukumomin tsaro sun zafafa matakan tsaro ta ko ina cikin birnin, da nufin kama masu kai wadan nan hare hare. Zuwa Yanzu babu hakikanin yawan mutane da suka jikkata ko rayuka da suka salwanta.

Birnin Maiduguri yana fuskantar karin tashe tashen hankula da ake aza laifin kan kungiyar Boko Haram wacce take auna galibin hare harenta kan jami'ai da hukumomin gwamnati.

Idan za'a iya tunawa bada jumawan nan bane,'yan Boko Haram suka dauki alhakin kashe kanin Shehun Borno.

XS
SM
MD
LG