Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Ingila Zasu Gurfanar Da Michael Adebolajo Gaban Kotu Ranar Litinin


Michael Adebolajo, a wani hoto da aka dauka a wni wurin zanga zanga.
Michael Adebolajo, a wani hoto da aka dauka a wni wurin zanga zanga.

‘Yansanda a Ingila sun gabatar da tuhuma kan mutum na biyu dangane da mummunar kisan da aka yiwa wani sojan kasar da ranar Allah kan titin birnin London cikin watan jiya.

‘Yansanda a Ingila sun gabatar da tuhuma kan mutum na biyu dangane da mummunar kisan da aka yiwa wani sojan kasar ido na ganin ido kan titin birnin London, cikin watan jiya.

‘Yansanda a birnin London suka ce an tuhumi Michael Adebolajo jiya Asabar kan kisan soja Lee Rigby ranar 22 ga watan mayu, da kuma wani yunkurin da yayi na neman kashe ‘Yansanda biyu.

Ranar jumma’a ne aka sako Michael daga asibiti sakamakon harbin bindiga da ‘yansanda suka yi masa a wurinda suka kashe sojan. Ana sa ran gurfanar da shi gaban kotu gobe litinin idan Allah ya kaimu.

Adebolajo shine dayan mutanen biyu ‘yan asalin Najeriya da ake zargi da kisan sojan Ingilan Rigby a kudu maso gabashin birnin, kusa da wani barikin soja. Dayan mutumin Michael Adebowale tuni aka tuhumeshi a farkon makon nan bayanda shima aka sako shi daga asibiti.

Dukkansu biyu sun gayawa mutane da suka taru a wurinda suka kashe sojan cewa sun dauki wannan mataki ne a matsayin ramuwar gayya kan kisan da sojojin Ingila suke yiwa musulmi a Iraqi da Afghanistan.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG