Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Turawa Bankuna Kudi - CBN


Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

A watan Maris kotun kolin Najeriya ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudaden naira har zuwa karshen 2023.

Babban bankin Najeriya ya ce ya turawa bankunan kasar takardun kudaden naira don su wadatar da al’umar kasar da ke fuskantar karancin kudi a hannunsu.

A ranar Juma’a bankin na CBN ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na Facebook inda ya kuma nemi bankunan da su yi aiki har a karshen mako don kudin ya kai ga hannun jama’a.

“CBN na ba da umurni ga bankuna da su loda na’urorin cire kudi da takardun naira, su kuma bude hanyar karbar kudaden a cikin banki har zuwa cikin karshen mako.” Mukaddashin shugaban sashen yada bayanai na bankin Dr. Isa Abdulmumin ya ce a cikin sanarwar.

‘Yan Najeriya sun kwashe tsawon lokaci suna fama da karancin takardun kudi tun bayan da aka sauya fasalin naira 200, 500 da 1,000 a bara.

Lamarin ya haifar da tarnaki ga harkokin kasuwanci a sassan kasar tun daga karshen shekarar da ta gabata.

A watan da ya gabata kotun kolin Najeriya ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudaden naira har zuwa karshen 2023.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG