Accessibility links

China Ta Mika Kukanta Ga Sudan Kan Garkuwa Da 'Yan Kasarta

  • Aliyu Imam

Wasu 'yan kasar China.

China ta mika kukanta a hukumance ga Sudan sabo da kama ma’aikata ‘yan kasar Sin su 29.

China ta mika kukanta a hukumance ga Sudan sabo da kama ma’aikata ‘yan kasar Sin su 29 da aka kama ana garkuwa dasu, daga nan ta tura wata tawaga zuwa Sudan din domin neman a sake su.

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Xie Hangsheng, ya gana da wani babban jami’in jakadanci na Sudan a Beijing a jiya talata, inda ya gabatar da kuka kan harin da ‘yan tawaye dake yankin suka kai kan wani kamfanin China dake aiki a kudancin Sudan a jihar Kodofan, ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ambaci Xie yana gayawa jami’in na Sudan Omer Eisa Ahmed, ya tabbatar da lafiyar ‘yan kasar Chinan da ake garkuwa dasu. Haka kuma ya gaya masa cewa China tana aza matukar muhimmanci wajen kare lafiyar ‘yan kasarta a ketare.

Xie, ya kuma yi kira ga Khartoum ta dauki matakai na kare lafiyar wasu ‘yan kasarta da kamfanoninsu a Sudan.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya kuma bada rahoton wata tawagar daga Chinan ta isa babban birnin Sudan din jiya talata domin neman sakin ‘yan kasar 29 da ake garkuwa dasu. Rahoton yace wani kakakin kungiyar ‘yan tawayen SPLA a Nairobin Kenya ya gayawa kamfanin dillancin labaran Xinhuan ta woyar tarho, cewa an kai ‘yan kasar Chinan 29 zuwa wani wuri da babu barazana ga ruwarsu kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.

Wani rahoto daga Sudan yace ma’aikata ‘yan kasar China su 18 sun tsere daga sansanin da aka kai musu harin suka doshi Khartoum.

Ahalinda ake ciki kuma Majalisar dinkin duniya zata tura wata babbar jami’a mai kula da ayyukan jinkai zuwa kudancin Sudan.

Cikin sanarwa da majalisar ta bayar jiya talata, tace Valerie Amos, karamar sakatare mai kula da ayyukan jinkai, zata ziyarci jihohin Equatoria da kuma Juba, daga laraban zuwa jumma’a.

XS
SM
MD
LG