Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'Yancin Biladama Ta Kalubalanci Gwamnati


Jami'an tsaro kenan ke sintiri.
Jami'an tsaro kenan ke sintiri.

Bayanai na nuna cewa cin hanci yayi kaka gida a harkokin hukumomin Najeriya na yau da kullum, kuma hakan na da nasaba da harkokin tsaron kasar.

Dan rajin hakkin bil adama na kungiyar Human Rights Watch, Awwal Rafsanjani, shine ya furta haka a tattaunawa da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa.

Wannan ya biyo bayan kalaman da wani mutum yayi, wanda yace shi sojan Najeriya ne, kuma har ma yayi karin haske dangane da yaki da kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram.

Rafsanjani ya kara da cewa cin hanci na daya daga cikin dalilan da yasa ake samun rashin nasara wajen kawar da ta’addanci.

Mr. Awwal ya kara da cewa "rahotanin dake fitowa, ba abin mamaki bane domin dama jama’a na hasashen haka, ganin yadda jami'an tsaron najeriya suka kasa shawo kan matsalar tsaro a Najeriya."

”Saboda akwai wadanda ake amfani da su a cikin jami’an tsaron ake kulla wannan cin hancin ake ta amfani dasu don su sami riba ko don su sami kudi ko kuma su sami wata bukata saboda tsaban sonkai da kuma rashin adalci ga jama’an kasa”, a cewar Mr. Rafsanjani.

Yace rashin adalci da kuma take hakkin bil adama ba zai sa a sami cigaba da zaman lafiya ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG