Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama Bom Ne Ya Tarwatsa Jirgin Rasha da Ya Fadi a Masar - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barrack Obama yace yana kyautata zaton cewan bomb ne ya tarwatsa jirgin nan na kasar Rasha, wanda ya fado a cikin satin da ya gabata a Masar, kuma ya hallaka ilahirin mutanen dake cikin sa su 224.

Shugaba Obama ya fada wa wani gidan Radio ne a jiya Alhamis yana cewa zasu dauki lokaci mai tsawo suna nazarin wannan al’amari.Yace zasu tabbatar cewa masu binciken su da masu tattara bayanan sirri, sun samu ainihin bayanin hakikanin abinda ya faru kafin su fidda matsayar su.

Sai dai yace ba shakka ga bisa dukkan alamu akwai abinda keda nasaba da bomb wajen hadarin wannan jirgin.

Shima Prime Ministan Birtaniya David Cameron yace ga bisa dukkan alamu jirgin nan ansa masa bomb ne.

Cameron ya fada jiya Alhamis a Landan sailin da suka hadu shi da shugaban na Masar Abdel Fatah el-sisi da kuma shugaban Rasha yace duk wani bayani cewa akwai bomb cikin jirgin nan zaici gaba da zama hasashe ne,dake da tasiri.

Shi dai wannan jirgin sanfurin Air Bus na camfanin Metrojet ya tashi ne daga Sharm el-Sheikh kuma yana kan hanyar sa ta zuwa St. Petersburg a ranar Asabar din data gabata, kafin ya tarwatse ya fadi a zirin Sinai.

Sai dai kungiyar ISIS ta dauki alhakin aikata wannan danyen aiki amma kuma kawo yanzu bata bada wata kwakkwarar hujjan da zaisa a gasganta hakan ba.

XS
SM
MD
LG