Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraqi sun kafa tutarsu a birnin Ramadi


Wani sojan Iraqi rike da tutar kasarsa a tsakiyar birnin Ramadi

Akwai tabbaci dakarun Iraqi sun shiga birnin Ramadi sun cafke gine--ginen gwamnati amma babu tabbas duk garin ya fada hannunsu

Jami'an sojojin Iraqi sun ce sun daga tutar kasar a ginin gwamnati dake birnin Ramadi, watanni bakawai bayan da mayakan ISIS suka cafke birnin wanda shi ne babban birnin yankin Anba.

To saidai akwai rahotanni dake karo da juna akan nasarar da sojojin suka samu kan birnin na Ramadi. Yayinda Birgediya Janar Yahaya Rasool ya bayyana a gidan talibijan din kasar yau Litinin cewa sun kubutar da Ramadi shi kuwa shugaban sojojin da suke yaki a Anbar Jamnar Ismail al-Mahlawi cewa ya yi har yanzu akwai wani bangaren garin da yake hannun 'yan ISIS.

Wani jami'in sojojin Amurka yace an fatattaki mayakan ISIS daga gine-ginen gwamnati amma ya ki ya tabbatar dakarun Iraqi sun kubutar da garin gaba daya..

Kawo yanzu babu wata sahihiyar majiya da ta tabbatar da yawan mutanen da suka jikata a yakin. Ba'a san fararen hula nawa ne suke birnin dake da tazarar kilimita dari daga yammacin Baghdad ba. Wani mai magana da yawun gwamnatin Iraqi yace yawancin mazauna garin sun fake a wani asibiti kusa da birnin..

A wani halin kuma sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare 29a sansanonin ISIS a makon da ya wuce cikinsu uku sun fada kusa da Ramadi daga ranar Lahadi zuwa Litinin din nan da suka jikata mayakan ISIS 12.

Kanal Steve Warren na sojojin Amurka dake yaki da ISIS yace tun watan Mayu Amurka da kawancenta sun kai hare hare 830 ciki da kewayen Ramadi kana sun horas da dakarun Iraqi da suka cafke birnin.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG