Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Isra'ila Sun Bindige Wani Bafalasdine Har Lahira Bayan da Ya Dabawa Mutane Uku Wuka


Wani jami'in tsaron Isra'ila bayan aukuwar harin wukan a July 26, 2018.
Wani jami'in tsaron Isra'ila bayan aukuwar harin wukan a July 26, 2018.

Dakarun Isra’ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira bayan da ya sulale ya shiga wani yankin yahudawa ya dabawa wasu mutane uku wuka.

Biyu daga cikin mutanen sun samu munanan raunuka, yayin da mutum na uku ya dan samu karamin rauni.


Dakarun na Isra’ila sun ce lamarin ya faru ne a unguwar da ake kira Adam, wacce ke tsakanin Birnin Qudus da garin Falasdinawa na Ramalla a yankin gabar Kogin Jordan.


Wannan rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawan, ya ta’azzara ne tun daga watan Maris, bayan da Falasdinawan suka fara bore a kullum a kan iyakar Isra’ila da zirin Gaza.


Akalla Falasdinawa 140 da kuma sojan Isra’ila daya suka mutu.
Tsageru daga yankin Gaza da ke karkashin ikon kungiyar Hamaz, sun harba rokoki zuwa yankin Yahudawa, lamarin da ya haifar da mummunan martani daga Isra’ilan

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG