Accessibility links

Dakarun Mali Dana Faransa Suna Dannawa Kan Birnin Gao

  • Aliyu Imam

Sojojin Faransa a wata tashar soji a Mali.
Yau jumma’a dakarun sojojin gwamnati da sojan Faransa ke rufawa baya sun ci gaba da dannawa yankin arewacin kasar da yan tawaye suka kama, yayinda aka shiga mako na 3 kenan da fara fattatakar”yan kishin Islama dake rike da arewancin kasar.

Jami’an soja sun ce hare-haren jiragen saman yakin faransa da aka yi cikin dare, ya kori mayakan sakan, wanda ya taimaka wa dakarun Faransa da na Mali ci gaba da kutsawa zuwa garin Gao inda yan gwagwarmayar islamar suka fi karfi, daga inda yan tawayen suka arce.

Yan tawayen sun kwace yawancin arewacin Mali watanni 10 da suka wuce, inda suka kafa tsatsaurar shari’ar musulunci wanda hakan ya kawo fargabar kasancewar wurin maboya ga yan ta’adda. Bayan da suka fara dannanwa kudancin kasar, faransa da tayi wa Mali mulkin mallaka a da, ta shigo cikin al’amarin bisaga rokon da gwamnatin Mali tayi.
XS
SM
MD
LG