Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Gudun Hijira Daga Habasha Ya Zama Kansila A Amurka


Oballa Oballa has been elected to the City Council of his adopted hometown of Austin, Minnesota. He is the first refugee, first immigrant and first person of color to serve on the council. (Photo courtesy Oballa Oballa)

An zabi Oballa Oballa a matsayin Kansila a garin da ya zabi zama, Austin, jahar Minnesota. Shi ne dan gudun hijira na farko, dan asalin wata kasa na farko kuma na farko wanda ba Bature ba da za zama dan Majalisar.

Tattakin da Oballa Oballa ya yi har zuwa ranar zabe, mai tsawo ne kuma wanda aka aza ba mai yiwuwa ba ne.

Ya tashi ne a yankin Gambella na kasar Ethiopia, inda ya shaidi kisar kiyashin da ya yi sanadin halakar kawunsa da wasu daruruwan mutane. Ya jure ma takawa da kafa ta tsawon makwanni biyu a mawuyaciyar hanya har zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kasar Kenya. Ya shafe shekaru 10 a sansanin, inda akasarin lokuta bai ma da abin ci.

Yanzu an zabe shi kansila a Majalisar Birni a garin da ya zabi zama, wato Austin na jahar Minnesota. Shi ne dan gudun hijira na farko, dan asalin wata kasa na farko kuma na farko wanda ba Bature ba da ya zama dan Majalisar birnin. Ya ce shi bai taba shakkar zai kai ga wannan matsayin ba.

“Ina matukar alfaharin kiran kai na dan kasar Amurka, inda zan iya hidima in kuma taimaka ma jama’a,” a cewarsa. Ya kara da cewa, “Game da batun cimma buri a Amurka kuwa, duk abin da na kallafa rai a kai, muddun na yi aiki tukuru, zan iya samu. Haka na fahimci batun cimma buri a Amurka.”

Oballa Oballa ya tashi ne a kasar Habasha kuma ya shafe shekaru 10 a sansanin ‘yan gudun hijira. Yanzu an zabe shi mamba a Majalisar Birni n agarin da ya zabi zama, wato Austin na jahar Minnesota. Shi ne dan gudun hijira na farko, dan asalin wata kasa na farko kuma na farko wanda ba Bature ba da ya zama dan Majalisar birnin.

Oballa na daya daga cikin sabbin Amurkawa ‘yan siyasa a kalla biyar masu alaka da Afurka wadanda su ka ci kujeru a birni, jaha ko ma matakin tarayya a zaben Amurka na ranar Talata.

Naquetta Ricks
Naquetta Ricks

Esther Agbaje ta zama Ba’amurkiya ‘yar Najeriya ta farko da aka zaba mamba a Majalisar Dokokin Jahar Minnesota, Oye Owolewa ya zama Ba’amurke dan asalin Najeriya da aka zaba karamin wakili a Majalisar Wakilan Amurka da ke birnin Washington D.C.

Ita kuwa Naguetta Ricks, Ba’amurkiya 'yar asalin kasar Liberia da ke Aurora, jahar Colorado, an zabe ta ne mamba a Majalisar Wakilan jahar ta Colorado. Omar Fateh kuwa, dan wasu bakin haure daga kasar Somaliya, an zabe shi ne mamba a Majalisar Dattawan jahar Minnesota.

Oballa ya kuduri aniyar shiga siyasa da zarar ya shiga Amurka a shekarar 2013. Ya zama shugaban majalisar daliban ta jami’ar yankinsa kana ya taimaka wurin yin doka a majalisar jihar da ta maganace karancin abinci a jami’o’in unguwanni.

Tun da yake yana hidima a unguwa, sai aka gane huskarsa yayin da yake zuwa kofa kofa yana neman kuru’u.

Yace a koda yaushe ina ina aikin sa kai. Idan ka je kasuwar Walmart zaka samu sunana a wurin, mutane da dama suna gane ni. A dan haka a lokacin da na yanke shawarar shiga takara mutane sun riga da sun gane huskata, abin da yasa kwamitin neman zaben ya samu komai cikin sauki.

Somalia born Omar Fateh candidate in Minnesota
Somalia born Omar Fateh candidate in Minnesota

Amma duk da haka yana bukatar hadin taimakon su ta hanyar tattaunawa dasu a kan batutuwa suka dame shi, kamar samar da makarantun kananan yara da gidaje masu saukin kudi da kuma ayyukan bunkasa tattalin arziki.

Ya ce “Dole na gabatar da kaina ba fada musu manufofina da kuma dalilin da yasa na shiga takara, saboda yakamata na fadawa masu kada kuri’a da mazauna unguwar cewa ni ne mutumin da na cancanta.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG