Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake ya Kutsa da Motar Boma-Bomai Cikin Ayarin Motocin NATO


NATO
NATO

Wani dan Taliban dan kunar bakin wake ya kutsa da motar boma-bomai cikin ayarin motocin NATO a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, ya hallaka sojoji uku 'yan kasashen waje, wasu biyar kuma sun ji ciwo.

Kungiyar NATO ba ta bayyana kasashen sojojin ba. Kakakin ma'aikatar harakokin cikin gidan kasar Afghanistan, Sediq Sediqi ya ce haka kuma wasu fararen hula goma sha uku sun ji ciwo.

Da safiyar Talatar nan harin boma-boman ya wakana a kan babban titin da ke tsakanin ofishin jakadancin Amurka da filin jirgin saman birnin Kabul.

'Yan sanda sun ce dan kunar bakin waken ya kai harin ne kusa da babbar kofar shiga ofishin jakadancin. Ba tare da bata lokaci ba 'yan Taliban suka fito suka yi ikirarin kai harin.

XS
SM
MD
LG