Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dandazon Jama'a ne ke Zanga-Zanga a Birnin New York


Masu zanga-zanga a New York
Masu zanga-zanga a New York

Zanga-zanga ta barke a fadin birnin New York jiya laraba, don maida murtani akan hukuncin da wasu mahukunta suka yanke na cewa ba za' a tuhumi wani dansanda bature, da ya makare wani bakar fata da baya dauke makami har sai da ya mutu a watan yulin da ya gabata.

Dandazon jama'a ne suka dunguma a birnin har gaban zauren times square, ‘yan sa’o’I kadan bayan da aka sanar da hukuncin. Yawan jama’ar ya sa ‘yan sanda suka tare hanyar shiga wani rukunin shagunan Rockefella dake kusa da wurin, inda aka shirya za' a yi bikin sanya kwaliyar kirsimeti da aka saba yi.
daruruwan mutane sun kwakkwanta a kasa inda suke nuna alamar mutuwa don abin da ya faru da Mr. Eric.

Wani mutum da ke wucewa, lokacin da kisan Mr. Eric Garner ya faru, ya dauki hoton bidiyon duk al’amarin da ya faru ta wayar sa inda shi marigayi Eric Garner dan shekaru 43 da haihuwa ke gardama da wasu ‘yan sandan birnin New York da suke kokarin kama shi bisa zargin aikata laifin saida wata taba. Bayan ‘yan mintoci kadan sai dan sanda Daniel Panteleo, ya damke shi, ya makure shi ta baya, ya kuma ingizashi wajen hanyar da ake wucewa.
Anji Mr. Garner mai kiba sosai, wanda ke fama da cutar daukewar lumfashi na nanata cewa lumfashin sa na dauke wa, “ ba fa ya ya iya lumfashi”. Likitocin da suka duba shi sun ce Mr. Garner ya mutu ne sanadiyar shakare mai wuya da aka yi, abin da hukumar ‘yan sandan birnin New York ta hana, a dokance a hekaran 1993.

XS
SM
MD
LG