Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Sake Cabawa


Donald Trump, dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican

An zargi dan takarar shugaban kasa na jami’iyar Republican Donald Trump akan murguda maganar da yayi jiya Talata akan yancin mallakar bindiga wanda yawancin mutane suke ganin yana karfafa tada rigima akan yar takarar Democrat Hillary Clinton


Ganin akwai gurbi a kotun kolin kasar wanda zai ba shugaba daman nada wasu alkalan kotun, Trump yace idan Clinton taci zabe, zata soke doka ta biyu dake ba Amurkawa yancin mallakar bindiga.


“Yace idan ta samu daman nada alkalan to ko baku da ta cewa. Kodayake jama’a wannan doka ta biyu kila tana nan amma ni ban sani ba”.


Bayan wasu sa’o’I sai Trump yace shi yana maganarsa ce da wata jam’iyar siyasa ce, yace babu wata fasara da za a yiwa kalaman nasa.


Amma kuwa manajan kampe na Clinton ya dauki wa’yannan kalaman Trump tamkar barazana


Manajan kampen Rooby Mook yace kalaman na Trump suna da hadari. Yace mutumin dake neman shugabancin kasar Amurka bai kamata ya rika ingiza mutane ga tashin hankali ta kowace hanya ba.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG