Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FARANSA: Sojoji Sun Yi Lalata da Yara Maza

Shugaban Faransa Francois Hollande

Ana zargin sojojin Faransa da yin lalata da yara maza 'yan shekaru daga 8-15 da haihuwa a kasar Afirka ta Tsakiya

A Faransa, hukumomin kasar suna binciken zargin sojojin kasar sunyi lalata da yara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayinda suna aikin kiyaye zaman lafiya a yankin a bara.

Jiya Laraba ma'aikatar tsaron kasar ta bada sanarwar cewa "hukumar kare hakkin Bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a karshen watan Yuli na shekarar 2014, ta sanar da gwamnatin kasar cewa yara sunyi zargin sojojin kasar sunyi lalata dasu".

Wata kungiyar 'yan raji mai fafutukar yaki d a cutar kanjamau tace ana zargin kimainin sojojin Faransa 16 da yin lalata da yara 10 maza 'yan shekaru 8-zuwa 15. Ana zargin sojojin da aikata haka ne a wani sansanin 'yan gudun hijira kusa da tashar saukar jiragen sama dake babban binrin kasar Bangui, tsakanin watan Disemba na shekarar 2013 zuwa watan Yuni na shekara ta 2014.

Idan har aka tabbatar da zargin, ma'aikatar tsaron kasar Faransar tace "zata yi hukunci mafi tsanani" kan sojojin da aka samu da laifi.

Zargin ya tada ayar tambayar kan take taken sojojin Faransa a wasu kasashe masu yawa wadanda ta yiwa mulkin mallaka. Ahalin yanzu akwai sojojin Faransa wadanda suke yaki da Boko Haram ta kan iyakokin Najeriya. Haka nan suna aikin kiyaye zaman lafiya a Ivory Coast, kuma suna samar da tsaro a wasu birane daga 'yan tawayen al-Qaida a Mali.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana fuskantar rikici na sabanin akida tun a shekara ta 2012, lokacinda 'yan tawaye musulmi wadanda suka juma suna fafatawa da gwamnati suka kifar da gwanatin kasar.

XS
SM
MD
LG