Wasu sun sha bayyana a wajen al'umma da sunan sun yi nadama tare da fita daga kungiyar Boko Haram, to amma a zaton wasu ma suna ganin cewa wasu sun bayyana tuban nasu ne saboda an tarwatsa su sun rasa mafaka sai su dawo gari su ce sun tuba.
Wasu daga cikin gudaddun suna komawa gaban iyayensu ne da ‘yan uwa da abokan arziki. Amma wasu jama’ar kuma suna ganin abin da yafi dacewa shine tarbiyyantar da tubabbun a ilimance ne mafita.
‘Yan Boko Haram dai sun zama babbar matsala a Najeriya, musamman ma a Arewacin kasar da ma makwabtansu. Sannan kullum hukumomin kasashen Afrika da abin ya shafa suna ta kokarin shawo kan lamarin da a mafiya yawan lokuta ake samun kwan-gaba kwan-baya.