Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Iceland ya yi murabus saboda boye kudi a kasar waje


Firayim Ministan Iceland Sigmundur David Gunnlaugsson saboda samunsa da boye kudi a kasar waje
Firayim Ministan Iceland Sigmundur David Gunnlaugsson saboda samunsa da boye kudi a kasar waje

Firayim Ministan Iceland ya yi murabus jiya Talata sakamakon gagarumar zanga zagar da ta biyo bayan tonon silili da aka buga da ya nuna cewa, ya zuba jari a kasashen ketare da nufin batarda sawun abinda ya mallaka.

Jiya shugaban kasar Olafur Ragnar Crimsson wanda ya katse ziyar da ya kawo nan Amurka ya koma gida, yaki amincewa da bukatar da Firayim Ministan Sigmundur David Gunnlaugsson ya gabatar na neman a rushe gwamnati, majalisa kuma ta nemi a gudanar da zabe kafin cikar wa’adin mulkinsa, bayan rahoton fallasa da aka buga da lakabi Panama Papers.

Firayim Minista Gunnlaugsson ya fuskanci matsin lamba da neman ya yi murabus daga dubban masu zanga zanga tunda aka fitar da rahoton da ya nuna shi da matarsa sun kafa wani kamfani tare da taimakon wani kamfanin lauyoyin Panama da dake da alhakin tonon sililin. Gunnlaugsson ya musanta aikata ba daidai ba, yace an biya harajin da ya kamata.

Gunnlaugsson yana cikin jerin ‘yan siyasa dari da arba’in da kuma jami’an gwamnati a fadin duniya da aka ambata a takardun Panama da ya sanya alamar tambaya a yiwuwar keta doka a fannin harkokin kudi.

Wadansu ‘yan kasashen Afrika da aka ambata a takardun sun hada da dan kawunan shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma, da ‘yar tagwayen shugaban kasar Jamhuriyar Congo Joseph Kabila, da tsohon gwamnan jihar Delta na Najeriya da yake daure, da kuma ministan kudin kasar Angola, kasa ta biyu dake tashen arzikin man fetir a Afrika bayan Najeriya..

XS
SM
MD
LG