Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministar Ingila Zata Kawo Ziyara Nan Amurka Wanan Juma'ar


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

A ranar Jumma'a mai zuwa ake sa ran Firayim Ministar Ingila Theresa May, zata zama shugabar wata kasa ta farko da zata ziyarci sabon shugaban Amurka Donald Trump, a mataki da zai kara tabbatar da abunda kasashen biyun suke kallo a matsayin dangantakar da bata misaltuwa.

Shugaban na Amurka yayi alkawarin gwamnatinsa zata-ma "kara kusantar Ingila" a danganatakar da ta shiga tarihi, kuma ya bayyana burinsa na sabunta- da-kuma karfafa danganataka tsakanin kasashen biyu, musamman bayan da Ingila ta fice daga kungiyar tarayyar turai.

Haka ita ma Firayim Minista Theresa May, tana da irin wannan buri na karfafa danganatakar da tuni take da karfi, musamman yayinda shugabar ta Britaniya take kokarin kulla sabbin kawance ta fuskar cinikayya bayanda kasar ta fice daga kungiyar tarayyar turai.

Masu lura da al'amuran yau da kullum suna hasashen yadda zata kasance idan shugabannin biyu suka gana a karon farko.

XS
SM
MD
LG