Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fulani Sun Wuce Wani Yanki Yayi Masu Rajista


Shuwagabanin kungiyar Miyetti Allahna Najeriya sun fara yin wani rangadi

A kokarin da take yi na kawo fahimta tsakanin makiyaya da manoma kabilar Yarbawa da Fulani, shuwagabanin kungiyar Miyetti Allah, na Najeriya, sun fara yin wani rangadi tare da yin taruruka da bangarorin da lamarin ya shafa dan lalubo bakin zaren.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Najeriya, Alhaji Muhammadu Kiro Ardon Zuru, ne ya jagoranci taron da akayi a Iseyin dake jihar Oyo. Ya ce matsalolin dake faru tsakanin Fulani, da kabilar Yarbawa shine yasa kungiyar ta je Pategi, dake jihar Kwara, aka zauna dasu da shuwagabanin Fulani, da na Nufawa, bisa ga matsalolin dake faruwa yauzu kuma muna zo Iseyin, saboda a tabbatarwa da Fulani, zaman su a kudu kuma su zauna lafiya kuma su kira yara domin a zauna lafiya kuma shuwagabaini Yarbawa su basu cikaken goyon baya da hadin kai domin Najeriya, kasa ce ta kowace kabila.

A batun yiwa Fulani makiyaya rajista kuwa cewa yayi “Mu bamu karbeshi ba kuma bamu yarda dashi ba domin al’umar Fulani, sun wuce wani yanki yayi masu rajista bazai yuba kuma ba zamu yarda ba kuma bazamu bada goyon baya ga wannan al’amari ba."

Shima sakataren manoma na karamar hukumar Iseyin, Isiyaka Olayinka, ya ce taron da akayi ya zama taron kwarai kuma manya manya sun halarta da yake taron mai mahimmanci ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

XS
SM
MD
LG