Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gada Ta Rutsa Da Mutane A Jami'ar Miami Ta Kasa Da Kasa Dake Florida


Gadar Jami'ar Kasa Da Kasa da ta rushe a Miami
Gadar Jami'ar Kasa Da Kasa da ta rushe a Miami

Gadar da aka gina domin taimakawa daliban Jami'ar Florida International University dake Miami Florida ta rushe kashe mutane hudu tare da jikata wasu guda takwas

Wata gada da ake bi da kafa wadda aka kammala ginawa da kwana daya a Miami, dake jihar Florida a nan Amurka ta rufta jiya Alhamis, kuma ta murkushe motoci.

Jami’an ‘yan sanda sunce tuni ake ta gudanar da ayyukan ceto a wannan wurin dake tsakanin babban harabar jami’ar kasa da kasa dake Florida, da kuma wurin kwanan dalibanta.

Motoci masu daukan kaya masu nauyi da tono kurakusai da ma karnukan ‘yan sanda suna cikin sahun abubuwa da ake ta anfani dasu wajen wannan aikin ceton.

Shugaban hukumar kashe gobara dake Miami, Dave Downey yace an samu gawarwakin mutane hudu da akan gadar da ta danne kana an kai wasu mutanen 8 asibiti.

Haka kuma ‘yan sanda sunce motoci 8 ne gadar ta danne.

An gina gadar ne da niyyar saukaka wa daliban jami’ar ta Florida yawan gitta titin dake gaban makarantarsu mai yawan samun cincirindon motoci, wanda sau tari tsallake shi yake zamewa wani jan aiki, domin ko layin motoci 8 ne ke gilmayya a lokaci guda

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG