Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gajiyar Mulkin Demokradiyya Da Ya Anfani Mutane A Jihar Ikko


Hedkwarat hada-hadar kasuwar hannu jarin kafanoni a Legas

Kafin gwamnatin Ikko ta yanzu, karkashin gadojin birnin tamkar wani matattaran yan tada zaune tsaye da masu shan tabar wiwi da 'yan fashi da makami ne.

Amma yau lamarin ya sake domin gwamnatin ta kakkabe duk karkashin wata gada a birnin ta kuma sabunta wuraren sun zama abun sha’awa.

Sai dai wasu musamman yan arewa masu kasuwanci a wasu karkashin gadojin lamarin bai yi masu dadi ba.

Wasun su sun yi asarar dukiyoyi har ma ya kai ga wasu barin birnin gaba daya. Sarkin Hausawan wuraren da abun ya shafa Alhaji Mustafa Muhammed ya ce sun yi babbar asara sakamakon korarsu da aka yi.

A ta bakinshi sun yi kusa da shekaru hamsin suna sana’a a wuraren. Ya ce suna biyan haraji na gwamnatin tarayya da na jiha da ma na kananan hukumomi.

Amma karam tsaye sai aka taso masu a ka ce su kwashe kayansu.

Duk da haka ta bangaren kula da lafiyar mutane sai a ce tubarkalla.

Mazauna Legas masu shekaru daga sittin da yara kasa da shekaru shida basa biyan ko sisin kwabo a asibitocin gwamnati ko wane irin aiki ko magani za’a basu.

Cinkoson motoci da aka san Legas da shi da yanzu babu. An yi gadojin tsallakawa a kan manyan tituna domin dakile yadda motoci ke kashe mutane yayin da suke ketare hanya.

A harkokin tsaro ma an samu cigaba. Sai dai har yanzu matsalar matasa da ke kiran kansu yan kasa da aka sani da sunan “area boys”” masu razana mutane har yanzu ta na nan.

Jihar Legas na daya daga cikin jihohin da suka fi samun kudin haraji. An kiyasta cewa jihar tana samun nera miliyan dubu ashirin da tara kowane wata.

Ta dalilin haka wasu suna ganin abun da gwamnatin ke yi bai taka kara ya karya ba idan an kwatanta da abun da take samu.

Idan har tana samun makudan kudade me yasa ta kasa shawo matsalar ambaliyan ruwa da take fama da shi da kuma rashin kula da karkara.

Ga karin bayani daga Ladan Ibrahim Ayawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG