Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi A Tunisia Sun Sami Lambar Yabo Ta Nobel


Houcine Abbassi, babban sakataren kungiyar kwadago ta Tunisia akeyiwa barka.

Sun Ceci kasar daga fadawa yakin basasa, bayan juyin juya hali data shiga.

An bada lambar yabo ta Nobel domin zaman lafiya ga gamayyar wasu kungiyoyi "saboda irin gudumawar da suka bayar na gina tafarkin demokuradiyya a Tunisia", bayan juyin juya halin da aka yi a kasar a shekara ta 2011 da aka kira ta Jasmine.

Kungiyoyi hudu ne suka hadu, wadanda suka hada da babbar kungiyar kwadago, kungiyar masu masana'antu, kungiyar masu rajin kare hakkin Bil'Adama, da kuma kungiyar lauyoyi.

Juyin juya halin da aka yi a Tunisia wanda ya kai ga hambare dadadden shugaban kasar dan kama kariya, shine dalilin wasu boren da aka yiwa wasu shugabanni da ake kallo a zaman 'yan kama karya a kasashen Masar, da Libya, Da Syria.

A cikin sanarwar da kwamitin Nobel din ya bayar jiya jumma'a, ya jinjinawa wadannan kungiyoyi da daidaita al'amura a kasar tana daf da fadawa cikin yakin basasa.

XS
SM
MD
LG