Accessibility links

Yawancin gidajen yarin Najeriya na bukatar kulawa, domin kusan dukansu tun lokacin mulkin mallaka aka ginasu, kuma babu abun da wata gwamnati tayi domin ingantasu.

Bayan an tabbatar cewa an dauki matakan da suka dace na rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya, su gidajen yarin na bukatar kulawa sosai kuwa.

Yawancinsu basu da wadatattun ma'aikata. Kayan aiki sun yi kadan matuka. Ababen bunkasa rayuwar 'yan gidan yarin babu su. Babu banbanci cikin gidajen yarin. Ko ina mutum yaje lamarin daya ne.

Kwanturolan gidajen yarin jihar Neja, Musa Miayaki yace a gaskiya basu da iasassun ma'aikata. Yace basu da isassun motoci da zasu rika kai masu jiran hukunci kotu. Ga kuma rashin ruwa ko kuma karancinsa. Haka kuma babu magani na kula da marasa lafiya.

Kwanturolan yayi wannan furucin ne a lokacin da ya karbi gudunmawar wasu kaya na bunkasa rayuwar 'yan gidajen yarin. Kayan sun hada dana yin welda dana aikin kafinta da duwatsun guga da kayan dinki da sauransu.

A karkashin shirin S.U.R.E.-P ne aka samarda kayayyakin da aka kaiwa firisinonin da yawansu ya kai dari biyar da sittin, dake cikin gidajen yari biyu a Minna fadar gwamnatin jihar ta Neja.

Alhaji Yusuf Haruna Kontagora shi ne daraktan kudi da ayyuka na shirin S.U.R. E.-P a jihar Neja, kuma yayi bayanin dalilin da yasa suka kai taimakon. Sun kawo kayan ne domin a koya wa masu zaman kaso sana'o'i idan sun gama wa'adinsu, zasu samu abun yi maimakon su koma aikata wasu laifukan da zasu yi sanadiyar komawarsu gidan yari.

Shi ma Malam Salisu Tanko limamin daya daga cikin gidajen yarin yace babu shakka idan an basu kayan aka kuma basu izini su koya, domin dama suna koyon to zasu karu. Ya ce a gidan yarin ya koyi karatu ya kuma saukar da Kur'ani Mai Girma. Yace yanzu litattafai ya keyi har suka dauki limancin gidan suka bashi.

XS
SM
MD
LG