Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwajin Makami Mai Linzami da Iran Tayi Ya Sabawa Dokar Majalisar Dinkin Duniya - Amurka


Makami mai linzami da Iran ta gwada ranar Lahadi

Fadar White House ta shugaban Amurka tace da alamu gwajin makami mai linzami da Iran ta gudanar a karshen mako ya sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

Kakakin fadar white Josh Earnest yace akwai "shaida mai karfi" da ta nuna cewa, hukumomin Farisa dake Tehran sun sabawa ka'idojin d a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shimfida dangane da makamai masu linzami.

Duk da haka kakakin na Fadar white yace wannan keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya, daban yake da yarjejeniyar da zata shiga tarihi da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran.

A ranar Lahadi ne Iran tayi bayanin cewa ta sami nasarar gwajin makami mai linzami da ta kera da kanta mai cin dogon zango , wanda tace linzaminsa zai kaishi har inda aka auna shi.

Ahalinda ake ciki kuma, majalisar dokokin Iran ta amince da kudurin da ya amince da yarjejenkiyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya shida kan shirin Nukiliyarta.

Kamfanin dullancin labarai na kasar IRNA yace, wakilan Majalisar Dinkin Duniya su 161 suka ce sun amince da dokaryayinda wakilai 59 suka ki. Wasu 13 suka kauracewa shirin baki daya.

A watan jiya ne majalisar dokokin Amurka ta kammala nazarin yarjejeniyar inda 'yan Democrat suka hana yunkurin da 'yan Republican suka so yi na kada kuri'ar nuna rashin amincewa da yarjejenyar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG