Accessibility links

Malam Isa Yuguda, yayi tur da wadanda suke yada abinda ya kira "jita-jitar" cewa wai yana neman kujerar mataimakin shugaban Najeriya a 2015

Gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi, ya karyata maganganun da wasu mutane da kafofin yada labarai a Najeriya suek bazawa cewar shi da gwamnan Jihar Katsina su na neman kujerar mataimakin shugaban Najeriya a zaben shekarar 2015.

A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, Malam Isa yuguda, yace shi babu abinda zai ce, sai dai "Allah Ya isa ga wadanda ke yada irin wadannan karairayin."

Haka kuma, yace bisa yardar Allah za a samu nasarar kokarin da ake yi na cimma zaman lafiya a Najeriya, musamman a arewa, ta hanyar kulla sulhu da 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati lid'dawati Wal jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram.

Ga martanin Malam Isa Yuguda ga tambayar da wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa yayi masa a kan ko da gaske ne yana neman kujerar mataimakin shugaban kasa:
XS
SM
MD
LG