Shugaba Buhari yace zai toshe duk wata hanya da mutane ke bi suna sace dukiyar jama'ar Najeriya.
Yayinda yake jawabi a taron ganawa da ya yi da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Indiya yace gwamnati zata kwato duk kudaden da aka sace kana zata gurfanar da duk wadanda aka samu suna da hannu cikin yin almundahana.
Shugaba Buhari yace kwato kudaden da gurfanar da wadanda suka sacesu zai zama daratsi ga duk wanda yake da niyar shiga gwamnati da nufin yin sata.
Shugaban ya tabbatarwa masu sauraronsa cewa ya san illar dake tattare da karkata dukiyar jama'a da yakamata a yi ayyukan cigaban kasa da ita zuwa asusun wasu daban ta hanyar da bata dace ba.
Yace zasu kwashi shekaru da dama suna yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Amma sun dukufa akan gina gwamnati ta gari mai adalci da zata dakile duk wata hanyar da ake anfani da ita ana sace kudaden kasar.
Saboda haka gwamnatin yanzu zata cigaba da gurfanar da wadan aka samu da laifin satar kudin kasa gaban shari'a tare da tabbatar cewa ana kwato kudaden domin ya zama kashedi ga duk wani dake shirin yin almundahana.