Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Taraba tana bin gwamnatin taraiya sama da naira biliyan 30


Farfesa Yemi Osinbajo Da Gwamna Darius Ishaku, a lokacinda mataimakin shugaban ke bude hanyar Jalingo-Kona-Lau
Farfesa Yemi Osinbajo Da Gwamna Darius Ishaku, a lokacinda mataimakin shugaban ke bude hanyar Jalingo-Kona-Lau

Gwamnatin jihar Taraba arewa maso gabashin Nigeria ta bukaci gwamnatin taraiya ta biya ta kudin da take binta, sama da naira miliyan talatin

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ba zata maida we kowace jiha kudin da ta kashe wajen kamalla manyan ayuka mallakar gwamnatin tarayya don kyautata rayuwar jama'a ba.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya ya furta haka yayin da yake bude hanyar Jalingo-Kona-Lau da gwamnati jihar Taraba ta gina lokacin da yake mai da martani ga bukatar gwamnatin tarayya ta mayar mata da kudi naira biliyan daya da miliyan dari uku da goma, da dubu dari shida da hamsin da biyar wajen kamalla aikin hanyar Jalingo- Kona- Lau mai tsawon kilomita ashirin da tara da gwamna Darius Dickson Ishaku yace ya kashe a jawabinsa sa lokacinda ake bude da hanyar.

Farfesa Osinbajo ya ce na gamsu da ayukan da gwamna Darius ya dukufa wajen aiwatarwa musamman a fannin gina hanyoyi da kyautata ayukan noma irin na zamani.

Gwamna Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba ya fadawa bakon nasa cewa daga watan mayun shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, ya yanzu gwamnatinsa ta kashe sama da naira biliyan talatin kan gina hanyoyi goma sha uku mallakar gwamnatin tarayya a garuruwa da kauyuka ashirin da biyu, kudaden da inji gwamnan idan aka maidawa jihar, zasu taimaka wajen samarwa jama'a muhimman abubuwan more rayuwa.

Baya ga aikin hanya, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da aikin sabuwar fasahar samar da ruwan fanfo mai anfani da katin ATM da manyan lambun zamani na Green House da jihar Taraba ta tanadar kan kudi naira biliyan shida da digo takwas da sama da naira biliyan biyu.

Gwamna Darius Dickson Ishaku ya yi wa muryar Amurka bayanin sabuwar fasahar samar da ruwan fanfon zai iya biyan bukatun mazauna Jalingo, masana'antu da kamfanoni nan da shekara ta 2030 yayin da ake sa ran, nan ba da jimawa ba za a soma jigilar kayan lambu ta jiragen sama zuwa manyan biranen Najeriya,

Wasu yan jihar ta Taraba sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan yunkuri. Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Taraba. Alh. Abdulrahaman Adamu shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa reshen jihar Taraba ya ce dimbin matasa za su amfana da ayukan yi da kuma bunkasa tattalin arzikin jiha.

Daga bisani mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Osinbajo ya yana da bangarorin da tashe tashen hankulan tsaunin Mambila ya shafa a asirce don neman hangar warware rikicin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG