Accessibility links

Gwamnatin kasar Siriya ta musanta cewa, mataimakin shugaban kasar ya koma bangaren adawa


Mataimakin shugaban kasar Siriya Farouq al-Shara
Gwamnatin Syria tace karya ne, labarin da ake bazawa na cewa wai mataimakin shugaban kasar Farouq al-Shara, ya gudu, ya bar gwamnatin ya koma bangaren ‘yantawaye.

Kan haka ne tashar Talabijin ta gwamnatin kasar ta fito tana ruwaito opishin M. Farouq, 73 kuma Musulmi mabiyin mazhabar Sunni, suna cewa koda wasa bai taba ko tunanin ya fice, ya bar kasar ba.

Haka kuma ofishin yayi marhabin da nadin da aka yiwa tsohon jigon diplomasiyar kasar Algeria Lakhdar Brahimi a matsayin sabon wakilin kasashen duniya wajen kokarin warware wannan matsalar.

Mr. Brahimi dai shine zai cike gurbin Kofi Annan, tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya, wanda a karshen wannan watan zai jingine wannan aikin.
XS
SM
MD
LG