Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Kafa Kwamitin Sabunta Dokokin Aikin Jarida


Shugabannin gidajen talibijan da radiyo a kasar Nijar

Aikin kwamitin din shi ne duba dokokin aikin jarida a kasar ta Nijar da zummar bada shawarwarin da zasu taimaka wajen yi masu gyaran fuska da zai zama daidai da aikin jarida a wannan zamanin.

Matakin ka iya taimakawa a kaucewa wasu dokokin da yanzu suke karo da juna a harkokin aikin jarida a cikin kasar.

Hajiya Fajimatu Gali Adam babbar magatakarda a ofishin ministan watsa labarai na kasar tace wasu dokokin tun lokacin mulkin mallaka suke ana anfani dasu. Wasu kuma sun yi shekaru biyar ko bakwai ana anfani dasu amma yanzu an gano suna da matsaloli. Tace dalili ke nan da aka yi tunanen kafa kwamitin da zai taimaka wurin yin gyaran fuska wa dokokin.

Inji Hajiya Fatima bayan kwamitin yayi nashi aikin daga baya sai a tara duk 'yanjarida kowa ya bada ra'ayinsa kafin a tantance a samu kundun tsarin dokokin aikin jarida daya na kasar.

To saidai yanzu daga cikin mambobi shida da kwamitin ya kunsa babu dan jarida ko daya tak abun da Ibrahim Haruna shugaban cibiyar 'yan jarida yace tamkar an yi tuya an manta da albasa ne. Lamarin ya sanya shakku a zuciyar 'yan jarida bisa manufar sauye sauyen dokokin aikin jarida a kasar da gwamnati take son yi.

A cewar wasu 'yan jarida idan an sa wani cikin kwamitin din wanda bai san aikin jarida ba yana iya kawo rudani. Kamata yayi a sa 'yan jarida cikin kwamitin a yi aiki dasu tun daga farko har karshe. Idan aka yi hakan kowa ya san za'a yi abun da yakamata. Suna ganin ba daidai ba ne bayan kwamitin ya gama aiki a kira 'yan jarida a basu kwana daya su duba domin su kawo gyara. Amma zai fi mahimmanci idan tare da 'yan jarida aka yi aikin.

Amma Hajiya Fatima tace babu wata muguwar manufa game da yunkurin yiwa dokokin aikin jarida gyaran fuska. Babu wani shirin cutar 'yan jarida.

A sakamakon korafe korafen na cibiyar 'yan jarida shugabannin kwamitin sun amince su shigo da 'yan jarida ukku cikin kwamitin. Bayan kwamitin ya gama aikinsa zai gabatar wa hukumar sadarwa ta kasa sakamakonsa.

Ga rahoton Souley Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG