Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Romania Ta Soke Dokar Ba 'Yan Siyasa Kariya daga Cin Hanci da Rashawa


Masu zanga zangar kin dokar da aka kafa

A Romania, bayan da aka kwashe kwanaki shida ana gudanar gagarumar zanga zanga, jiya Lahadi jam'iyyar RSD mai mulkin kasar ta soke dokar da zata baiwa 'yan siyasa kariya daga fuskantar shari'a saboda cin hanci da rashawa.

Wannan matakin da gwamnatin Firayim Minista Sorin Grindeanu ta dauka, ya biyo bayan zanga zangar da dubun dubatan 'yan kasar wadanda suka cika dandalin Nasara, wadda ake ganin sune mafiya girma na nuna kyamar gwamnati, rabon da kasar ta ga irin wannan- tun a shekarar 1989,lokacinda gwamnatin shugaban kasar, Nicolas Ceausescu ta fadi.

Dokar wacce majalisar ministcoin kasar ta amince da ita cikin daren Talata, da zata kare jami'ai daga fuskantar shari'a idan kudaden da suka sata basu kai dalar Amurka dubu 47, da 800 ba, watau Naira milyan 21, da dubu dari biyar da 10.

Gwamnatin kasar ta dage cewa akwai bukatar aka kafa wannan doka domin a rage cunkoso a gidajen fursinar kasashen da cin hanci d a rashawasuka yi musu katutu.

XS
SM
MD
LG