Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hakan Ya Tamakawa Tattalin Arzikin Amurka


Barack Obama da Joe Biden

A jibi Juma’a ne dai sabon shugaban Amurka Mr Donald Trump, zai karbi ragamar shugabancin kasa daga hannun shugaba mai barin gado Barack Obama.

Muryar Amurka, tayi waiwaye akan wasu daga cikin alkawuran yakin neman zabe da shugaba Obama ya cimma da kuma darrussan koya daga ‘yan Afrika.

Batun tada komadan tattalin arziki ta hanyar samarda aiyuka da kyautata ilimi, da kimiya da fasaha da kuma kiwon lafiya mai inganci na daga cikin abubuwan da shugaban ya nanata alkawarinsa akansu a lokacin yakin neman zabe.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyar siyasa da diflomasiya, a jami’ar, Bayero kano, yayi tsokaci game da rawar da Gwamnatin Obama, ta taka game da alkawari ta fuskar tsaro a duniya, yace tashe tashen hankali da rigiggimu a duniya ba raguwa suka yi ba amma dai dama shima yana cikin kamfe din daya yi cewa idan ya ci zabe zai rage Sojojin amurka, dake waje.

Koda yake bai ragesu kamar yadda ake zato ba amma yayi kokari ya rage, sanan kuma batun Gwantanamo Bay, wannan shima har yanzu da akwai saura, amma yayi kokari ya rarrage, kuma gaskiya wannan ya taimaka mashi ta fuska dayawa.

Domin ya tamakawa tattalin arzikin Amurka, saboda irin kudaden da take sawa a zaunar da Sojojinta a kasashen waje, kuma ya kara masa ta gomashi a wajen mutane a cikin gida, ya kuma rage bakin jini da Amurka, tayi a kasashen waje.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:51 0:00

XS
SM
MD
LG